Dillalan man fetur din a Najeriya sun bayyana cewa sun dakata kan cece-kucen da ake yi game da farashin mai na matatar man Dangote kamar yadda kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL ya fitar a ranar Litinin.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kasuwar ta man fetur din suka bukaci matatar ta Dangote ta bayyana farashin man fetur da ta sayar wa kamfanin na NNPCL saboda ayi gaskiya da gaskiya.
'Yan kasuwar sun kara da cewa kasar ba za ta iya dogaro da albarkatun man fetur na cikin gida don gamsar da abin da take ci a kullum ba wanda ya kai Naira miliyan 50 bisa ga bayanan da Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya ta Najeriya Midstream/ Downstream ta gabatar.
Shugaban Kungiyar Masu sayar Kayayyakin Man Fetur PETROAN a kasar, Billy Gillis-Harry da Shugaban Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya, Abubakar Maigandi ne suka yi wannan bukata a wata tattaunawa ta daban da suka yi da jaridar DAILY POST a ranar Litinin.
Sa'adda shugaban kungiyar dillalan man fetur din na kasa Alhaji Abubakar Mai gandi ya bayyana cewa kungiyar IPMAN ba ta da masaniya dangane da cewa da akeyi sun gwammaci sayo man daga kasashen ketare kamar yadda aka saba.
Sai a latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI