Kungiyar Dattawan arewa a Najeriya ta yi Allah wadai da kisan Sarkin Gobir

Kungiyar Dattawan arewa a Najeriya ta yi Allah wadai da kisan Sarkin Gobir

An dai sace basaraken gargajiyar ne tare da dansa a ranar 18 ga watan Agustan shekarar 2024, inda daga bisani aka kashe shi duk da neman kudin fansa da ƴan bindigar suka yi daga hanun iyalansa.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa dauke da sa hannun Farfesa Tukur Muhammad-Baba, babban sakataren kungiyar tuntuba ta Arewa ACF da Abdul-Azeez Suleiman, daraktan yada labarai na kungiyar dattawan Arewa NEF, sun bukaci da a gudanar da bincike tare da nazari mai zurfi kan tsare-tsaren harkokin tsaron kasar domin ganin an yaki wannan matsalar ta ta'addanci tare da kawar da ita baki ɗaya.

Sannan kungiyar ta ACF ta mika sakon ta'aziyya ga iyalai da abokan arziki na marigayin da  gwamnatin jihar Sakkwato da kuma Majalisar Sarkin Musulmi bisa aika-aikar ta ƴan ta’adda.

Kana ta bukaci gwamnati da hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya tare da dukkanin masu ruwa da tsaki da su hada karfi da karfe wajen samun kawar da matsaloli da suka shafi na tsaro da kuma tabbatar da ganin doka da oda na aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)