A wani jawabi da ya yi ta kafar radio da talabijin ɗin ƙasar ɗazunann, shugaban kasar ya ce ya ji taƙaicin asarar rayuka da dukiyoyi da zanga-zangar ta haifar, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki da su dakatar.
“Ina matukar bacin rai da asarar rayuka da aka yi a jihohin Borno, Jigawa, Kano, Kaduna da dai sauransu, da barnata kayayyakin jama'a a wasu jihohin, da yadda ake wawushe manyan kantuna da shaguna, sabanin alkawarin da masu shirya zanga-zangar suka yi na cewa za a yi zanga-zangar cikin lumana”.
Shugaban ya ce irin wannan ɓarnar da aka yi mayar da ƙasar baya ce, domin za a sake amfani da ƙudade wajen gyara su.
Inda ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu yayin zanga-zangar.
Mista Tinubu ya ce a matsayisa na shugaban ƙasar, dole ne ya tabbatar da zaman lafiya, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada na kare rayuka da dukiyoyin kowane dan kasa, don haka gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen barin wasu tsiraru masu manufa ta siyasa su wargaza wannan kasa.
Tinubu, wanda ya ce gwamnatinsa a shirye ta ke ta saurara tare da magance matsalolin masu zanga-zangar, ya tabbatar da cewa ya ji kiran nasu da babbar murya.
"Ina kira ga masu zanga-zangar da masu shirya zanga-zangar da su dakatar da duk wata zanga-zangar da kuma samar da taga don tattaunawa”
Batun dawo da tallafin mai
Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen ganin an samar da shugabanci nagari ga ƴan Najeriya.
Shugaban ya kare matakin da ya ɗauka na cire tallafin man fetur daga hawarsa karagar mulki, yana mai cewa, Tinubu ya ce, duk da cewa matakin cire tallafin man fetur ya yi tsauri da tasiri ga ƴan Najeriya, amma hakan ya zama dole domin tuni matakin ya haifar da mai ido ga tattalin arzikin ƙasar da kuma kawo cikas ga wasu dake amfana da ita.
Shugaban ya bayar da hujjar cewa jimillar kudaden shiga da gwamnati ke samu ya ƙaru da fiye da ninki biyu, inda ya kai sama da N9.1tn a farkon rabin shekarar 2024 idan aka kwatanta da na shekarar 2023.
Ya ci gaba da cewa, sannu a hankali ana samun karuwar aiki a bangaren da ba na mai ba, tsabanin yadda aka dogara da man kadai a baya.
Don haka, Tinubu ya yi kira da a yi hakuri, yana mai cewa, “Tattalin Arziki yana farfadowa;
Wargaza demokradiyar Najeriya
“Yanzu da muka shafe shekaru 25 muna jin ɗadin mulkin dimokuradiyya, kada ku bari makiya dimokuradiyya su yi amfani da ku wajen cimma burinsu na saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasar nan wadda za ta mayar da mu baya kan tafiyarmu ta dimokuradiyya.
Duk da bai kama suna ba, ana ganin shugaban na martani ne kan yadda ake neman maida zanga-zangar ya koma goyan bayan Rasha kamar yadda aka gani a wasu ƙasashen yammacin Afirka.
A ranar Asabar din da ta gabata, hotuna da bidiyo na masu zanga-zanga a Kano tare da ɗaga tutar ƙasar Rasha sun yi ta yaɗuwa yayin da masu zanga-zangar ke rera wakar da harshen Hausa cewa, wajen kira ga Rasha ta cece su.
Daruruwan matasa masu karancin shekaru sun bukaci shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da ya sa baki a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya dorawa jami’an tsaro aikin wanzar da zaman lafiya da bin doka da oda a kasar, daidai da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙsa na kare hakkin dan Adam, wanda Najeriya ta rattaba hannu a kai.
"Tsaro da tsaron dukkan 'yan Najeriya su ne mafi muhimmanci," in ji shi.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta saki sama da Naira biliyan 570 ga jihohi 36 domin jin daɗin ƴan kasa baƙi ɗaya da more rayuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI