Kotun kolin Najeriya ta kori karar da ke neman a rushe hukumar EFCC

Kotun kolin Najeriya ta kori karar da ke neman a rushe hukumar EFCC

Jihohi 19 da suka shigar da karar gaban kotu sun hada da Kogi, Kebbi, Katsina, Sokoto, Jigawa, Enugu, Oyo, Benue, Anambra, Plateau, Cross River, Ondo, Niger, Edo, Bauchi, Adamawa, Taraba, Ebonyi, kuma Imo.

Ko da yake jihohin Ogun da Nasarawa sun kalubalanci yadda ake tafiyar da harkokin NFIU ne, inda suka bayar da shawarwarin a yiwa sashen sauye-sauye.

Yayin yanke hukunci, alkalan kotun mai mabobi bakwai, karkashin jagorancin, mai shari’a Uwani Abba-Aji, sun kori karar ne saboda rashin kwararan hujjojin da aka gabatarwa kotun.

Mai shari’a Abba-Aji ta ce korafe-korafe shida da masu gabatar da kara suka gabatar gaban kotun basu da ma’ana.

A cewar kotun, dokar da ta samar da hukumomin cin hanci da rashawar, sai da aka dukkanin ka’idojin da kundin tsarin mulki ya tanada, wanda hakan ne ya bawa majalisar dokokin kasar amincewa da samar da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)