Alƙalin kotun mai shari’a Emeka Nwiter ne ya bada umarnin bayan da lauyan hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati EFCC R.U. Adagba ya sanar da kotun cewa gwamnatin Najeriya ta janye tuhumar da takewa Gambaryan.
Lauyan na EFCC ya ce dalilin da ya sa aka ɗauki wannan mataki na da alaƙa da yanayin lafiyar Gambaryan da kuma rawar da alaƙar ƙasa da ƙasa ta taka.
Hukumar EFCC ta gurfanar da shugaban kamfanin Binance a babbar kotun tarayya gaban mai shari’a Emeka Nwita a ranar 8 ga watan Afirilu.
An gurfanar da shi kan tuhuma 5 dake da alaƙa da kuɗi da safarar kuɗi da bisa ka’ida ba da batun haraji.
A baya kotun ta yi watsi da buƙatar beli da aka nema na shugaban kamfanin na Binance har karo 2.
Bayan kammala sauraron lauyan EFCC alƙalin kotun mai shari’a Nwite ya sallami shugaban kamfanin Binance Tigran Gambaryan tare da amincewa da janye tuhumar da ake masa.
Alƙalin ya kuma daga shari’a tsakanin gwamnati da kamfanin hada-hadar kudin Binance zuwa ranar 22 da ranar 25 ga watan Nuwamba don ci gaba da sauraron ƙarar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI