Wata gamayyar ƴaƴan jamiyyar APC da suka fito daga arewa ta tsakiyar Najeriya ne suka shigar da Ganduje ƙara da jamiyyar APC da hukumar zabe ta Najeriya INEC.
Kungiyar ta buƙaci a haramta naɗin da aka yiwa Ganduje na shugabancin jamiyyar saboda hanyar da aka bi wurin naɗin ya ci karo da dokokin jamiyyar.
Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya kori wannan kara bisa dalilai da ya zayyana lokacin da yake yanke hukunci
Mai shari’a Ekwo a lokacin da yake yanke hukunci ya ce gamayyar ƴaƴan jamiyyar APC da suka fito daga arewa ta tsakiyar Najeriya ba su da hurumin shigar da wannan ƙara.
Alkalin ya ƙara da cewa gamayyar kungiyar da ta shigar da ƙarar ba ta yi amfani da hanyoyin cikin gida ba wurin magance matsalar cikin kafin ta kai batun gaban kotu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI