Kotu ta gayyaci Yahaya Bello kan sabon zargin wawure naira biliyan 110

Umurnin dai ya biyo bayan karar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa EFCC ta shigar, inda take neman a gurfanar da tsohon gwamnan da wasu mutane biyu a gaban kuliya bisa zargin almundahana da naira biliyan 110.

EFCC na tuhumar Yaya Bello da Umar Shuaibu Oricha da Abdulsalami Hudu da kashe sama da Naira biliyan 110 na dukiyar al’umma wajen mallakar wasu kadarori a Abuja da Dubai.

Sabbin tuhume-tuhumen dai na zuwa ne daidai lokacin da tsohon gwamnan ya ki halartan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ake tuhumarsa kan sace zunzurutun kudi har N80.2bn lokacin da yake rike da madafun iko a jihar Kogi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)