Kotu ta dakatar da hukumar VIO daga cin tarar masu ababen hawa a Najeriya

Kotu ta dakatar da hukumar VIO daga cin tarar masu ababen hawa a Najeriya

Haka nan kotun ta umarci jami’an hukumar na VIO su daina tsaida masu ababen hawa akan hanyoyin ƙasar.

Mai shari’a Evelyn Maha ce dai ta yanke wannan hukuncin, bayan da Abubakar Marshal, mai rajin kare hakkin bil’adama ya shigar da ƙara kan lamarin.

A hukuncin nata ta ce, kotun ta gamsu da hujjojin mai ƙara na cewa babu wata doka da ta baiwa waɗanda ake ƙara hurumin tsaidawa da kamawa da kwacewa ko kuma cin tarar masu ababen hawa a kan hanya.

Mai shari’a Maha ta kuma bada umarnin dakatar da waɗanda ake ƙara, daga tauye haƙƙin ƴan Najeriya na yin zirga-zirga yadda suke suke so ba tare da sahalewar doka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)