Kotu ta dakatar da gudanar da zaben ƙananan hukumomi a jihar Kano

Kotu ta dakatar da gudanar da zaben ƙananan hukumomi a jihar Kano

Mai shari’a Simon Ameboda ne ya dakatar da hukumar gudanar da zaben da ake shirin yi a jihar.

A hukuncin da alƙalin kotun ya yanke ya ce naɗin da aka yi na shugabancin hukumar zabe a jihar da sauran shugabbanni ya saba da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, saboda suna ɗauke da katin jamiyyar NNPP.

Alƙalin ya ce naɗin shugabannin hukumar ya saba da sashi na 199(1) da sashi na 200(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yiwa gyara a 1999.

Har wa yau kotun ta ce naɗin ya saba da sashi na 4(b) na dokokin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano.

Kotun tace hukumar zabe a yanzu ba za ta iya gudanar da zabe ba, duba da yadda aka karya ƙa'idojin naɗin shugabannin hukumar.

Kotun ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC kada ta bawa hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano KANSIEC kayan da za ta yi amfani da su wurin gudanar da zabe har sai an bi dukkanin dokoki da ƙa’idoji wurin samar da shugabancin hukumar.

Kafin hukuncin kotun na yau an shirya yin zaben ƙananan hukumomin jihar Kano ne a ranar Asabar mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)