Kotu ta bukaci Janar Mohammed ya gurfana a gabanta

Kotu ta bukaci Janar Mohammed ya gurfana a gabanta

Wannan bayyanar ita ce za ta zama ta biyu da Janar Mohammed zai yi a gaban kotu domin bada shaida, a shari'ar da ta dauke hankalin jama'a da ake bukatar ganin kotu ta yi adalci a ciki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar, tun bayan fara sauraron ƙarar mutanen da ake zargi da aikata kisan gillar da aka yiwa tsohon babban hafsan sojin, sau ɗaya aka saurari ba'asin Janar Mohammed wanda ya yi aikin binciko gawar tsohon hafsan, a wani tsohon rafin da aka yi aikin haƙar kuza a Du dake Ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

Motar Janar Alkali da aka jefa ruwa bayan hallaka shi Motar Janar Alkali da aka jefa ruwa bayan hallaka shi rfi hausa

A wata hirar da ya yi da Jaridar Daily Trust kwanakin baya, Janar Mohammed wanda tuni ya yi ritaya daga aikin soji, ya ɓukaci kotu da ta yi adalci wajen kammala shari'ar da kuma hukunta wadanda ake zargi da hallaka tsohon babban hafsan sojin.

Tsohon kwamandan ya gabatar da sunayen wasu mutane a cikin wancan hirar, wadanda ya bayyana su a matsayin wadanda ke da hannu cikin kisan gillar.

Ita dai wannan shari'ar ta daɗe ana ɗage ta, abinda ya kai ga ritayar alkalin da ya fara sauraronta Daniel Longji a shekarar 2019.

Sai dai kafin ya aje aikin alkalancin, sanda ya bada belin mutane 27 da sojoji suka kama saboda zargin suna da hannu a kisan gillar, wato a tsakanin watan Disambar shekarar 2018 zuwa Fabarairun shekarar 2019.

Yanzu haka shari'ar na gaban Alkali Arum Ashom wanda ya gayyaci Janar Mohammed domin amsa tambayoyi a gabansa a ranar Alhamis mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)