Kotun tarayyar ta bada belin Yahaya Bello kan uɗi Naira Miliyan 500. Belin ya biyo bayan tuhumar da ake masa kan badaƙalar kuɗi biliyan 82.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bada belin yau juma’a bayan muhawarar da lauyoyin masu ƙara da wanda ake ƙara suka tafka a gaban kotu.
Mai shari’a Emeka ya bada umarnin lauyoyin wanda ake ƙara da su gabatar da mutum 2 da za su tsayawa Yahaya Bello, kuma ya kasance sun mallaki gida a inda kotun take da hurumi.
Kotun ta kuma umarci Yahya Bello ya gabatar da Fasfo ɗinshi tare da ci gaba da zama a gidan yari na Kuje har zuwa lokacin da zai cika sharuɗɗan beli.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI