Kotu ta bada umarnin tsare mata tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello

Kotu ta bada umarnin tsare mata tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello

Mai shari’a Maryanne Aninih ce ta bada umarnin tsare Yahaya Bello a hannun hukumar EFCC har nan da 10 ga watan Disambar mai zuwa, bayan taƙaddamar da akayi tsakanin lauyoyin da ke kare ɓangarorin biyu kan buƙatar badashi beli.

Lauyan da ke kare tsohon gwamnan Joseph Daudu, ya shaidawa kotun cewa dukkanin laifukan da ake tuhumar tsohon gwamnan na Kogi, laifukane da ake bada beli a kansu.

To sai dai lauyen da ke kara masu ƙara Kemi Pinheiro ya kalubalanci hakan, inda ya ce tun a ranar 22 ga watan Nuwamban nan ne aka shigar da buƙatar bada belin Yahaya Bello, lokacin kuma ba a gurfanar da shi ba.

Ita dai hukumar EFCC na zargin Yahaya Bello da wasu tsofaffin jami’an gwamnatin jihar Kogi biyu Abdulsalami Hudu da Umar Oricha, da amfani da kuɗin jihar da suka kai naira biliyan 110.4 wajen sayen wasu kaddarori a biranen Abuja da kuma Dubai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)