Kotu ta aike da masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya gidan yari

Kotu ta aike da masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya gidan yari

A zaman kotun na ranar Litinin din nan da mai shari'a Emeka Nwite ya jagoranta, ya bada umarnin kai mutane 9 daga cikin wadanda aka gurfar da su a gaban kotun wadanda maza ne gidan yari na Kuje, ya yin da ragowar macen ita kuma a kaita gidan yari na Suleja.

An dai gurfanar da mutanen ne bisa zarginsu da aikata laifuka 6 ciki kuwa harda cin amanar kasa da kokarin yiwa kasa zagon kasa da kuma tunzura mutane, wanda hakan ya sabawa sashi na 97 na dokokin Penal Code.

Sai dai bayan karanto kunshin tuhumar da ake musu, dukkanin wadanda ake tuhumar sun musanta zargin da ake musu.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 1 ga watan daya gabata ne matasa a Najeriya suka fara gudanar da zanga-zangar nuna dawa da halin matsin rayuwar da ake ciki a kasar, inda suka zargi gwamnatin shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu da daukar wasu matakai da suka haifar da hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)