Kamfanin mai suna Zhongshan ya dauki matakin ne sakamakon soke kwangilar da gwamnatin jihar Ogun ta bashi domin gina mata tashoshin shigar da kayayyaki daga kasashen ketare. Kamfanin ya ce gwamnatin Ogun ta saba ka'idar kwangilar da ta kulla da shi, saboda haka take neman diyya.
A sanarwar da ya gabatar yau, mai taimakawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kan harkokin hulda da jama'a Bayo Onanuga, ya zargi kamfanin da yi wa gwamnatin Najeriya karya a gaban kotun da ya kai kara Paris domin karbe jiragen fadar shugaban kasar da ake yiwa gyara yanzu haka a Le Bourget dake Paris.
Onanuga ya ce ministan shari'ar Najeriya da gwamnatin Ogun na shirya takardun kalubalantar matakan da kamfanin ya dauka a gaban kotu na kwace jiragen saman fadar shugaban kasar guda 3. An bayyana wadannan jirage guda 3 da suka hada da Dassault Falcon 7X da Boeing 737-7N6/BBJ da Airbus A330-243.
Mai bai wa shugaban kasar shawara ya ce suna da hujjojin dake tabbatar da cewar kamfanin ya yaudari kotun Faransa wajen gabatar da bukatarsa na karbe jiragen fadar shugaban kasar, saboda haka zasu bi matakan shari'a wajen karbo su.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da gwamnatin Najeriya ke fadawa cikin irin wannan dambarwa ba, wadda ke kaiga samun hukuncin kotun kasashen duniya a kan ta saboda sabawa yarjejeniyar kwangiloli.
Na baya bayan nan shine rikicin gwamnatin kasar da P&ID wadda ta kusan durkusar da Najeriyar kafin daga bisani ma'aikatar shari'ar kasar ta samu nasara lokacin da ta daukaka kara.
Wani abin takaici shi ne yadda ake amfani da wasu 'yan Najeriya wajen samun irin wannan hukunci a kan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI