Ɗaya daga cikin jami'an agaji da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa RFI Hausa cewa, sun tattara alkaluman mutane 100 da suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyar wannan ambaliyar ruwan.
Kodayake alkaluman sun saɓa da waɗanda gwamnati ta fitar da ke nuna cewa, mutane 37 ne kacal suka rasa rayukansu.
Kazalika RFI Hausa ta tattauna da Shugabar Gidauniyar Advocacy For Human Value, Fatima Mohammed Habib wadda ta ce, babu wanda ya san ainihin adadin mutanen da suka rasa rayukansu, duba da girman matsalar ambaliyar ruwan.
Fatima wadda gidauniyarta ta shafe tsawon kwanaki uku tana aikin agaji a Maidugurin, ta bayyana cewa, wannan ambaliyar ruwan ta shafi kashi 98 cikin 100 na al'ummar birnin Maiduguri, sannan kimanin mutane miliyan 7 ne matsalar ta shafa a cewarta.
Ku latsa nan domin kallon tattaunawar da muka yi da ita kai-tsaye a shafinmu na Facebook
Fatima ta ƙara da cewa, akwai wurare da dama da aka gaza kai musu agaji ballantana a ceto su saboda yadda ruwa ke neman shanye kawunan masu aikin agajin, yayin da mutane da dama suka koma kwana a can saman rufin gidajensu.
Akwai mutane da ke fama da yunwa, ya kamata gwamnati da ƙungiyoyin farar hula su rika samar da abinci ga mutane- inji Fatima.
Wasu hotunan bidiyo sun nuna yadda sojojin Najeriya da wasu jami'ai ke bada ɗauƙin gaggawa ta hanyar ceto waɗanda suka maƙale tare da raba abinci ga jama'a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI