Da yake jawabi a wajen wani taro da aka gudanar da Daura a ƙarshen mako, gwamna Radda ya ce ƴan bindiga ba za su iya gudanar da ayyukansu cikin walwala ba, fa ce tare da hadin gwiwar wasu ɓatara gari a cikin al’umma.
Malam Dikko Radda ya ce gwamnatinsa a shirye take ta tallafa wa jama’a domin taimaka wa jami’an tsaro wajen kare al’umma daga hare-haren ƴan fashin daji masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.
Domin cimma wannan muradun gwamna Dikko ya ce sun bullo da wani shirin ɗaukar matasa masu ƙokarin kare al’ummominsu domin basu horo da sauran kayan aiki da suke bukata domin tinkarar ƴan bindiga.
“Mun bullo da wani shiri wanda duk wata al’umma da ke shirye ta kare kanta, za mu ba su goyon baya da horon da ya dace don tinkarar masu aikata laifuka kafin zuwan jami’an tsaro.”
Gwamna Radda ya bayyana muhimmacin jajircewar al’umma domin ta kare kanta saboda, wasu kauyuka kafin jami’an tsaro su isa, bata gari za su iya cin karensu kuma su fice, inda ya bada misali da wata ziyara da ya kai wani kauye.
“Na je wani kauye mai suna Tsamiyar-jino, sai da na kwashe sa’o’i biyu kafin na isa duk da cewa da mota kirar jeep.Don haka, idan ƴan bindiga suka kai hari irin wadannan wuraren, daga lokacin da ka sanar da jami’an tsaro, za su ɗauki sama da sa’o’i biyu kafin su iya amsa kiran da ake yi musu, kafin zuwan jami’an tsaro za su iya yin duk abin da za su yi, Za su kashe mutane kuma sun yi garkuwa da wasu.
Dikko Radda ya jaddada cewa wannan yakin ba na jami’an tsaro ne su kadai ba, sai da taimakon al’umma, saboda ƙarancinsu.
“Na sha fada cewa jami’an tsaro ba za su iya yin wannan aikin su kadai ba. Ba ma da wadatar su. Ina mamakin yadda muke mutuwa ta wulakanci. An gaya mana cewa duk wanda ya mutu don kare iyalinsa zai shiga aljanna”.
“Za ka ga wasu miyagu guda biyar suna kai hari ga al’ummar 2,000 zuwa 3,000, suna yi wa ƴaƴa mata fyade, da kuma sace wasu ba tare da wata arangama da mutanen wannan unguwar ba. Idan akwai matasa 100 a cikin al’umma da suka tunkare su, ba za su yi harbi sama da sau uku ba tare da an kama su da hannu ba.
“Biyan kudin fansa ba ya ma hana ƴan bindiga kashe wanda aka yi garkuwa da shi. Wani lokaci sukan ƙarbi ƙudin su kashe wanda suka kama.”
Masu taimakawa ƴan bindiga da bayanai
Gwamnan ya ce hatta shugabannin al’umma suna hada kai da ƴan fashi domin kai hari ga al’umma domin neman ƙudi.
“Akwai wakilin hakimin kauyen da ya karbi Naira 700,000 daga hannun ƴan bindiga ya ba su damar shiga yankinsa suka kashe kusan mutane 30,” inji gwamnan.
"Akwai mata da aka kama, da kuma wani malami da ke aiki a matsayin mai ba wa ƴan bindiga bayanan sirri, a gaskiya, kusan dukkanin sassan mutane suna da hannu a wannan aikin."
Jami'an tsaron al'umma
Radda ya ce gwamnatinsa ta kirkiro da jami'an tsaro na al'umma don kare mazauna yankin.
“Mun horar da su tare da hada su da ƴan sanda da sojoji don yin aiki tare bayan mun ba su bindigogi, riguna masu sulke, da takalma da sauransu,”
Gwamnan ya ce sun bai wa jami’an tsaron babura 700 da motocin Hilux guda 65 da kuma motocin yaki masu sulke (APC) guda 10.
Motocin sulke da gwamnatin Katsina da ke arewacin Najeriya ta bai wa jami'an tsaro © Dikko Radda PHD“Muna biyan Naira miliyan 3 wajen samar da man fetur da kuma kula da wadannan motocin da ke sintiri zuwa kananan hukumomi , sai kuma Naira miliyan 1.5 ga marasa galihu da kuma Naira 750,000 ga sauran kananan hukumomin”
“Mun kuma sayi na’urorin hangen nesa na zamani da ba za ku iya samu a ko’ina a cikin kasar nan ba. Namu mai fasahar 5G kuma ba 3G da aka saba gani ba ne."
Jihar Katsina dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ƴan bindiga suka addabi jama’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI