Ministan lantarki na Najeriya Adebayo Adelabu ne ya faɗi haka lokacin da yake zayyana irin nasarorin da ma’aikatarshi ta cimma cikin shekara guda, a wani bangare na shirye-shiryen bikin cika shekara 64 da samun ƴancin kan ƙasar.
A jawabin da ya fitar ranar Lahadi, Adebalu ya alaƙanta nasarar ƙaruwar hasken lantarki da sauran ci gaba da ake samu a ma’aikatar da yake jagoranta da ƙoƙari shugaban ƙasar Bola Tinubu.
“Babban ci gaban da muka samu a yau shine. muna samar da lantarkin da ya kai Megawatts 5,500, tare da rarrabawa kuma hakan ke bawa kaso 40 na masu amfani da lantarki damar samun wuta ta awa 20 a koda yaushe a faɗin Najeriya”
“Idan kun lura an samu ci gaba sosai daga sanda muka zo wannan kujera zuwa yanzu, kuma mun yi shirin ƙara habbaka lamurra” a cewar Adebayo
Ministan lantarkin na Najeriya Adebayo Adelabu ya lissafa ci gaba da dama da fannin wutar lantarki ke samu a ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI