Kara farashin man fetur zai haɓɓaka tattalin arzikin Najeriya - Tinubu

Kara farashin man fetur zai haɓɓaka tattalin arzikin Najeriya - Tinubu

 

Shugaba Tinubu wanda ke ganawa da ƴan Najeriya a birnin Beijing na China jim kaɗan da kammala wasu sabgogin da suka kai sa ƙasar a hukumance, ya ce, ya zama tilas a ɗauki matakin ƙara farashin litar man domin haɓɓakar tattalin arzikin Najeriya.

 

A yayin ganawarsa da ƴan Najeriyar mazauna China, shugaba Tinubu ya ce,

Najeriya na kan samar da sauye-sauye, kuma muna ɗaukar tsauraran matakai da ba a taɓa ganin irinsu ba. Misali, za ku rika samun labari daga gida game da farashin man fetur.

Shugaban ya ɗiga ayar tambaya kan ko Najeriya za ta iya cimma gaci kuwa a fannin ci gaba kamar China muddin ba a ɗauki tsauraran matakai ba?. Yayin da ya bada misali da kayayyakin more rayuwa da China ke da su da suka haɗa da kyawawan hanyoyi da wadatacciyar wutar lantarki mara yankewa da tsaftataccen ruwan sha da makarantu masu inganci.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa, burinsu a matsayinsu na shugabannin Najeriya, shi ne su gadar wa yaran da ke tasowa a ƙasar yanayi mafi kyawu da za su yi tinkaho da shi.

Wannan na zuwa ne bayan Kamfanin Mai na NNPCL na Najeriya ya ƙara farashin lita guda na man fetur zuwa naira 855 daga naira 568.

Su kuma ƴan kasuwa na sayar da lita guda tsakanin naira 930 zuwa 1,200 a gidajen mai daban-daban a faɗin Najeriya.

Tun lokacin da shugaba Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur a watan Mayun 2023, al'amura suka fara rincaɓewa ga ƴan Najeriya, lamarin da ya haddasa tashin farashin kayayyaki tare da ruguza kananan sana'o'i.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)