Kar Najeriya ta kuskura ta janye tsarinta na tattalin arziki - Bankin Duniya

Kar Najeriya ta kuskura ta janye tsarinta na tattalin arziki - Bankin Duniya

Janye tallafin man fetur da kuma rushe tsare-tsaren hada-hadar kuɗaɗen ketare, na cikin sabbin sauye-sauyen tattalin arziki da wannan gwamnatin ta Bola Ahmed Tinubu ta fara aiwatar da su a tashin farko.

Sai dai dubban ƴan Najeriya na ci gaba da caccakar sabbin tsare-tsaren na gwamnatin Tinubu, a yayin da da gwamnatin ke ci gaba da jajircewa kan cewa, lallai abin da take yi shi ne kaɗai mafita ga ƙasar wadda ke cikin ƙangin talauci.

A lokacin da shugaba Tinubu ya ɗare kan karagar mulki, ana sayar da litar man fetur a kan naira 198, amma a yanzu farashin ya zarta naira dubu 1 sakamakon janye tallafin man.

Kazalika shugaba Tinubu ya ƙarbi ragamar ƙasar nan a lokacin da ke sayar da dala guda a kan naira 600, amma a yanzu ana sayar da dala guda a kan naira 1,700.

A yayin da yake magana a taron ƙaddamar da wani rahoto kan ci gaban Najeriya a birnin Abuja, darektan Bankin Duniya a Najeriya, Dr. Ndiame Diop ya bayyana cewa, akwai buƙatar ƙasar ta ci gaba da aiwatar da tsare-tsarenta duk kuwa da cewa, suna wahalar da ƴan ƙasar.

Diop ya yi gargaɗin cewa, janye  waɗannan tsare-tsaren ka iya zama musiba ga Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)