
Ƙudurin Majalisar ya biyo bayan amincewa da amsa kiraye-kirayen jama’a kan buƙatar dakatar da batun karin harajin da hukumar NCC ta sanar da shirin yi.
NCC ta sahalewa kamfanonin sadarwar su aiwatar da ƙarin kuɗin daga ranar litinin, kuma tuni kamfanin sadarwa ta MTN da ta kasance mafi girma a Nijeriyar ta kara nata firashin, saidai ya zuwa yanzu sauran kamfanonin sadarwar da su ka haɗa da Glo da Airtel da kuma 9mobile ba su bayyana sabon firashin da su ka aiwatar ba.
Ƙarin da MTN ta yi na kuɗin data da kwastamominta ke siya sun haɗa da na naira 1,000 da a yanzu ya koma naira 1,500, toh saidai a maimakon 1.5gb da aka saba samu, kamfanin ya ƙara datan zuwa 1.8gb.
Har ila yau kuɗin data na 15gb da ake siyarwa a kan naira 4,500 ya haura zuwa naira 6,000, yayin da datan 20gb ya haura daga naira 5,500 zuwa naira 7,500.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI