Kamfanin NNPCL ya ƙara farashin litar man fetur zuwa Naira 897 a Najeriya

Kamfanin NNPCL ya ƙara farashin litar man fetur zuwa Naira 897 a Najeriya

Wannan kari da NNPC ya yi na nuna cewar a yanzu za’a na sayan lita guda kan naira 897 daga farashin naira 617 da aka saba saya a baya.

Wannan farashin da aka ƙara ya nuna cewar an samu ƙarin sama da naira 250 kan kowacce lita.

Tuni bayanai ke nuna yadda jama'a suka shiga damuwa saboda ƙarin a jihohin ƙasar, musamman Kano da rahotanni ke cewa ana sayar da duk lita kan sama da 1000.

A jihar Lagos jama’a sun gaza samun man tun bayan sanarwar bisa matakin rufe gidajen mai da aka fuskanta a wasu wurare yayin da wasu ƙalilan ke sayar da man na fetur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)