Kamaru ta buɗe Madatsar Lagdo: Jihohin 11 Najeriya su shirya wa ambaliya - Gwamnati

Kamaru ta buɗe Madatsar Lagdo: Jihohin 11 Najeriya su shirya wa ambaliya - Gwamnati

Darakta-Janar na Hukumar NIHSA, Umar Mohammed, ya sanar cewa a ranar Talata Kamaru ta bude dam ɗin Lagdo — a daidai lokacin da ambaliya ta yi barna sosai a sassan Najeriya.

Ta baya-bayan na ita ce ta Maiduguri, wadda ta shafi sama da mutane miliyan daya ta shanye kashi uku bisa hudu na birnin.

Umar Mohammed ya ce hukumarsa za ta riƙa lura da yanayin tafiyar ruwan Madatsar Ruwa ta Lagdo, domin sanar da ’yan Najeriya inda aka kwana domin guje wa ambaliya.

A cewarsa, duk da cewa babu alamar samun babbar ambaliya a Najeriya a sakamakon hakan, amma ya kamata hukumomi da gwamnatoci a dukkan matakai su kasance cikin kyakyyawan shirin ko-ta-kwana.

Ya jaddada cewa jihohin da ya kamata su kasance cikin shiri sosai domin kauce wa tasirin ruwan Madatsar Ruwa ta Lagdo da za a sako su ne: Adamawa, Taraba, Kogi, Nasarawa, Binuwai, Anambra, Bayelsa, Delta, Edo, Kuros Riba da kuma Ribas.

Lagdo wata katafariyar madatsar muwa ce da ke Arewa Jamhuriyar Kamaru, da ke turo ruwa zuwa  Kogin Bibuwai, mai faɗin 586km2.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta bayyana cewa ruwan Madatsar Ruwa ta Lagdo da aka sako a 2022 ya haddasa mummunar ambaliya a Najeriya, wafda ta kashe mutane 693, ta raba miliyan 1.4 da gidajensu.

Mutane 2,400 kuma sun jikkata bayan ga gidaje 82,035 da gonaki masu faɗin hekta 332,327 da ta lalata.

A 2023 ma an samu irin haka, lamarin da hukumar NIHSA ta zargi gwamnatin Kamaru da rashin sanar da da Najeriya, sai bayan kwanaki bakwai da bude dam ɗin.

A watan Oktoba 2023 Majalisar Dattawa ta umarci Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da ta sake waiwayar aikin gina Madatsar Ruwa ta Dasin Hausa da sauran madatsun ruwa da za su taimaka wajen ɗauke ruwan da Kamaru take sakowa daga Madatsar Ruwa ta Lagdo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)