Jaridar ta ce babu dalilin danganta dimokiradiya da kama karya, kamar yadda ba za su iya zama wuri guda ba a Najeriya.
Wani sharhi na musamman da Jaridar ta yi, ya bayyana takaicin 'yan Najeriya a kan yadda jami'an tsaron farin kaya na DSS suka yi dirar mikiya a ofishin kungiyar SERAP da ke fafutukar ganin an samar da shugabanci na gari, saboda kawai ta yi Allah wadai da yadda kamfanin NNPCL ya kashe sama da dala miliyan 25 wajen gyara matatun mai daga shekarar 1999 zuwa yanzu, kuma har ya zuwa wannan lokaci babu guda dake aiki a cikin su.
SERAP ta kuma bukaci shugaban kasa da ya yi amfani da ofishinsa wajen tilasta NNPCL da ya rage kudin man fetur daga naira 855 zuwa naira 600 da aka sani.
Premium Times ta kuma bayyana yadda hukumar DSS ta kama shugaban kungiyar kwadago ta DSS Joe Ajaero a tashar jiragen saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja a ranar 9 ga watan nan na Satumba, lokacin da yake kan hanyarsa ta tafiya London domin halartar taron kungiyar kwadago ta duniya.
Sufeto Janar na Yan sanda Olukayode Adeolu Egbetokun © Nigeria PoliceJaridar ta kuma bayyana yadda jami'an tsaron suka kama matasan da suka shiga zanga zangar tsadar rayuwa, wadanda kotu ta bada belinsu a kan kudi naira miliyan 10 kowanne mutum guda bayan sun kwashe kwanaki a tsare.
Premium Times ta ce wadannan kama karya da gwamnatin Tinubu ke aikatawa bai tsaya haka ba, domin ya shafi kafofin yada labarai, inda a watan fabarairu sojoji suka kama babban wakilin tashar talabijin na Galaxy, Dele Fasan tare da sanya masa ankwa saboda daukar hotan masu zanga zanga a Owerri, baya ga Madu Onuorah mawallafin Global Upfront da Daniel Ojukwu na Cibiyar Binciken kwakwaf da Dayo Aiyetan, babban daraktan Cibiyar Binciken Kwakwaf da kuma Nurudeen Akwasika da Adejuwon Soyinka wadanda duk 'yan jaridu ne da suka dandana kudarsu, saboda yadda jami'an tsaro suka azabtar da su a karkahsin gwamnati Tinubu.
Jaridar ta kuma kara da cewar wakilinta Abdulkareem Mojeed da wasu abokan aikinsa guda 3 daga wasu kafofin yada labarai sun tsallake rijiya da baya lokacin da 'yan sanda suka bude musu wuta da harsasai a motarsu kusa da filin wasan MKO Abiola dake Abuja lokacin da ake zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.
Jaridar ta ce abin takaici ne shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi suna wajen fafutuka da kuma yaki da shugabanci mara inganci, tare da jagorancin adawa da mulkin soji da kuma bukatar rage farashin mai lokacin shugaba Goodluck Jonathan, a yau shi ke kauda kan sa ana amfani da kama karya wajen musgunawa jama'a.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa © Sawaba RadioPremium Times ta ce a matsayin Tinubu na daya daga cikin fitattun mutanen da suka yi adawa da gwamnatin mulkin sojin Janar Sani Abacha da ta kai ga tuhumarsa da laifin cin amanar kasa a shekarar 1994, bai dace ya dinga kokarin rufe bakin mutanen dake adawa da gwamnatinsa ba, ko kuma wadanda ke furta kalaman da suka sabawa manufofin gwamnatin sa.
Jaridar ta ce ganin yadda ba'a fayyace harkokin gwamnati a bainar jama'a, kamar yadda ake tafiyar da harkokin man Najeriya da yadda manyan jami'an gwamnati ke kece raini da kudaden talakawa, babu wani kama karya da zai rufe bakin jama'ar da karin farashin mai da cire tallafinsa tare da karya darajar naira ya yiwa illa, ganin yadda matakan suka jefa jama'a zuwa cikin kuncin talauci da rashin makoma mai kyau.
Jaridar ta karkare da cewar, kama karya a dimokiradiya zai dinga gamuwa da rashin amincewar jama'a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI