
A wata sanarwr da ya wallafa a matsayin shagube ga gwamnati mai ci, Atiku ya ce a 'yan shekarun baya an samu rahotannin dake nuna cewar dabbobi daban daban sun laƙume kudaden jama'a da aka warewa wasu ma'aikatu domin gudanar da ayyuka, saboda haka yace ya zama wajibi a ɗauki kwararan matakan kare dukiyar jama'a.
Tsohon mataimakin shugaban ya ce hakkin gwamnati ne ta dauki ƙwararan matakai domin ganin wadannan maƙudan kuɗaɗen da aka warewa bangaren lafiya ba su salwanta ba, duk da ƙorafin da ya yi cewar, gwamnati bata yiwa jama'a cikakkun bayanai ba akan hanyoyin da za ta bi wajen kashe wadannan kuɗaɗe.
Atiku ya tabbatar da buƙatun inganta ƙananan asibitocin karkara domin samarwa jama'a irin kulawar da suke bukata, saboda haka yana da muhimmanci gwamnatin ta yi bayani ga jama'a akan hanyoyin da za ta bi wajen kashe wadannan makudan kuɗaɗe dan ganin basu fada hannun gara ba.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce la'akari da cewar wadannan kuɗaɗe da aka ware domin kula da lafiya za su fito ne daga rancen da ƙasar zata karɓa, yana da muhimmanci gare ta, da ta yi cikakken bayanin inda aka ciwo bashin da kuma abinda aka yi da su.
Atikun ya kuma bayyana cewar yaudara ce yadda gwamnatin taki bayani dangane da aiwatar da manyan ayyuka a kasafin kuɗin daga wadannan maƙudan kuɗaɗe da za'a kashe.
Tsohon mataimakin shugaban wanda ya zargi gwamnatin ƙasar da rashin gaskiya wajen gudanar da ayyukan jinƙai, ya ce jama'ar Najeriya ba za su aminta da rashin gamsassun bayanai dangane da kasafin kudin ba, yayin da ya kuma zargi gwamnatin da ci gaba da yiwa jama'a karya dangane da halin da manyan asibitocin ƙasar ke ciki.
Atiku ya ce babu tantama gwamnatin Tinubu ta gaza a bangaren kula da lafiya saboda rashin samar da isassun kuɗaɗen da ake bukata, yayin da har yanzu cututtuka irin su zazzabin cizon sauro da tarin fika da ƙanjamau ke zama manyan cututtukan da ake fama da su a ƙasar.
A ƙarshe, tsohon mataimakin shugaban ya ce muddin da gaske gwamnatin Tinubu take yi wajen bada fifiko a ɓangaren kula da lafiya, to ya zama wajibi ta yiwa jama'ar kasar bayanin yadda za ta kashe kuɗaɗen da ta ware dalla dalla.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI