Jonathan ya bukaci 'yan Najeriya da kada su yankewa kasar kauna

Jonathan ya bukaci 'yan Najeriya da kada su yankewa kasar kauna

Jonathan ya ce har yanzu akwai kyakyawar fatar ganin mafarkin samarwa Najeriyar ci gaban da take bukata ya tabbata, kamar yadda shugabannin farko suka yi wajen dasa tubalin ginin kasar.

Yayin da yake tsokaci a kan bikin cika shekaru 64 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, Jonathan ya ce a daidai lokacin da jama'ar Najeriya ke jinjinawa shugabannin farko, ya na da muhimmanci a mayar da hankali wajen bada gudumawar da ake bukata domin habakar kasar.

Tsohon shugaban yace a karon farko an kwashe shekaru 25 ana gudanar da dimokiradiya ba tare da matsala ba, tun bayan kawo karshen mulkin soja a shekarar 1999, kuma matakin ya bada damar samun ci gaban tattalin arziki da hadin kan jama'a da kuma dorewar kasar a matsayin dunkulalliyar kasa.

Jonathan ya ce duk da yake ana fuskantar wasu manyan kalubalen da suka hana kasar samun ci gaban da take bukata ta fuskar tsaro da tattalin arziki, ya na da matukar muhimmanci a karfafa hukumomin kasa wadanda za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da samar da tsaro da kuma gudanar da karbaben zabe.

Tsohon shugaban ya kuma bukaci masu rike da madafun iko da su tabbatar da gaskiya da adalci a kowanne mataki, musamman wajen raba mukamai da arzikin kasa, tare da bai wa matasa damar shiga ana damawa da su.

A karshe tsohon shugaban ya bukaci 'yan Najeriya da su kaucewa yankewa kasar kauna wajen tunanin cewar ba za'a iya shawo kan wadannan matsalolin da suka yi wa kasar dabaibayi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)