Rahoton ya ce ya tattara alkaluman nasa ne a tsakanin gidaje dubu 7 da 707, daga jihohin Filato da Sokoto da Kano da Bauchi da Kwara da Oyo da Akwa Ibom da Ekiti da kuma Enugu.
Hukumar ƙididdigar Najeriyar ta ƙara da cewar, ta gudanar da binciken nata a tsawon kwanaki 17, daga 19 ga watan Afrilun da ya gabata zuwa 5 ga watan Mayun wannan shekara.
Rahoton ya nuna kashi 19.4 na gidajen da aka gudanar da binciken na amfani da Gas din girki ne a cikin kwanaki 30, inda akalla ko wannensu ke kashe naira dubu 10 da dari 239 da kobo 7 wajen siyen makamashin.
Jihar Sokoto ce ta daya wajen siyen makamashin da tsada, inda kowane gida daga cikin gidajen da aka yi binciken ke kashe naira dubu 12 da dari 439 da kobo 3, sai kuma jihar Enugu da ke biye mata da naira dubu 11 da dari 852 da kobo 2.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI