Babban shagon sayar da kayayyaki na Pick n Pay na Afika ta Kudu ne kamfani na baya-bayan nan da ya sanar da ficewarsa daga Najeriya saboda rashin kyawun tsare-tsaren tattalin arziki.
Yayin da yake jawabi shugaban kamfanin Sean Summers ya ce kamfanin bashi da wani zabi illa ya fice daga Najeriya ya kuma sayar da kaso 51 cikin 100 na hannun jari ga masu buƙata a cikin gida.
A shekarar 2016 ne kamfanin na Pick n Pay ya shiga Najeriya yayin da yayi haɗin gwiwa da kamfanin A.G Leventis wanda shima ke da manyan shagunan sayar da kayayyaki a sassan ƙasar.
Shekarar 2021 ne lokacin da kamfanin ya fara bude manyan shagunan sayar da kayayyaki musamman a manyan birane irinsu Legas da birnin tarayya Abuja.
Yanzu bari mu duba kamfanonin ƙetare da suka fice daga Najeriya daga 2020 zuwa yanzu, kamar yadda ƙididdigar jaridar Punch ta ƙasar ta wallafa.
2020:
Kamfanin Standard Biscuits Nigeria Ltd ne ya fara ficewa a wannan shekara, sai
-NASCO Fiber Product Ltd da
-Union Trading Company Nigeria PLC
- Deli Foods Nigeria Ltd
2021:
Haka abin yake a shekarar 2021, inda sannu a hankali tattalin arzikin kasar ke dada tabarbarewa, lamarin da ke barin kamfanonin ba tare da wani zabi ba illa ficewa.
Kamfanin Tower Aluminium Nigeria PLC ne ya fara ficewa a wannan shekara, sai
-Framan Industries Ltd
-Stone Industries Ltd -
-Mufex Nigeria Company Ltd
-Surest Foam Ltd
2022:
Shekarar 2022 ma ba’a barta a baya ba, inda kamfanin Universal Rubber Company Ltd da kamfanin
-Mother’s Pride Ventures Ltd da
-Errand Products Nigeria Ltd
-Gorgeous Metal Makers Ltd.
2023:
Shekarar 2023 ce lamarin yafi munana, inda lamarin ya fi ƙamari, yayinda tattalin arzikin ke ƙara fadawa cikin mawuyacin hali.
Kamfanonin da suke fice daga kasar a wannan shekara sun hadar da Unilever Nigeria PLC da
-Procter & Gamble Nigeria sai
-GlaxoSmithKline Consumer Nigeria Ltd da kuma babban
-ShopRite Nigeria
-Sanofi-Aventis Nigeria Ltd da
-Equinox Nigeria da kuma
-Bolt Food & Jumia Food Nigeria.
2024
To ko a bana ma an ga makamancin ficewar kamfanonin ketare daga Najeriya daga watan Janairu zuwa Octoban da muke ciki, inda kamfanoni irin su
-Microsoft Nigeria
-Wani bangare naTotal Energies Nigeria
-PZ Cussons Nigeria PLC da kamfanin
-Kimberly-Clark Nigeria sai
-Diageo PLC.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI