Janar Yakubu Gowon, wanda ya sadaukar da kai wajen hada kan kasa Najeriya

Janar Yakubu Gowon, wanda ya sadaukar da kai wajen hada kan kasa Najeriya

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci bikin, tsohon mataimakin shugaban kasa, Abubakar Atiku, ya bayyana tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Janar Yakubu Gowon, a matsayin mutum mai tsafta kuma maras cece-kuce tare da sadaukar da kai ga hadin kan kasa da mutunci.

Tsohon Shugaban Najeriya Yakubu Gowon Tsohon Shugaban Najeriya Yakubu Gowon RFI Hausa

An bayyana hakan ne a cikin wani sakon taya murna da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya fitar domin murnar cikar Gowon shekaru 90 da haihuwa. Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, ya yabawa Gowon a matsayin babban jigo wanda ya nuna hazakar shugabanci,da hazaka wajen tafiyar da al’amura da suka hada da yakin basasar Najeriya. Atiku ya kuma yaba masa bisa bullo da kungiyar masu yi wa kasa hidima ta kasa, wanda a cewarsa ya samar da hadin kan kasa, ta hanyar bai wa matasa daga al’adu daban-daban damar yin mu’amala da wasu da ba a yankinsu ba.

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya © Atiku Abubakar

“Abin farin ciki ne, hukumar NYSC ta yi nisa wajen karfafa auratayya, ta yadda za ta wargaza shingayen nuna kyama ga al’adu da kabilanci da addini. "Hakazalika, Gowon ya taka rawa wajen kafa kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, wadda ta taimaka wajen hada kan tattalin arziki da siyasa a yankin," in ji shi. Ya kuma yabawa tawali’u da rikon Amana na Gowon, inda ya ce tawali’u da saukin sa na daga cikin kyawawan halaye da ake girmama shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)