A sakon da ya aike domin bikin cika shekaru 90 da Gowon ya yi, Kanar Dangiwa ya ce akwai darussa da dama da ya dace shugabannin yanzu su yi koyi da shi daga rayuwar tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya na 2.
Dangiwa ya ce lokacin da aka yiwa Janar Gowon juyin mulki a ranar 29 ga watan Yulin shekarar 1975, yana halartar taron shugabannin kasashen Afirka ta OAU a Kampala dake kasar Uganda, amma nan take ya yiwa manema labarai jawabin amincewa da kawar da gwamnatinsa tare da fatan alkhairi ga shugaban da ya gaje shi, wato Janar Murtala Muhammad, inda ya kira jakadan Najeriya a London Alhaji Sule Kolo domin gabatar da bukatarsa.
Tsohon gwamnan ya ce a lokacin uwargidan shugaban kasar Victoria Gowon na London domin sayayya a lokacin da ake karya farashin kayayyaki, saboda haka ya bukaci jakadan da ya fitar da ita daga otel din da take zama, saboda ba shi da kudin da zai biya mata, inda nan take Kolo ya shaidawa fadar shugaban kasa, abinda ya sa Murtala ya bada umarnin a biya mata duk kudin da take bukata na zama a otel din.
Shugaba Bola Tinubu da Janar yakubu Gowon © Premium TimesKanar Dangiwa yace a Kampala Janar Gowon ya bukaci jakadan Najeriya ya saya masa tikitin zuwa London, bayan ya bada umarni a dawowa Najeriya da jirgin shugaban kasa, inda labarin ya kai ga shugabannin dake halartar taron a Kampala tare da Gowon, kuma nan take daya daga cikin su ya yi tayin bada jirginsa domin a kai shi London, ya yin da sauran kuma suka tara masa kudi bayan sun gano ba shi da komai a asusun ajiyarsa.
Tsohon gwamnan ya ce makwanni bayan juyin mulkin, sai aka ga Janar Gowon a layin sayen abinci a Jami'ar Warwick, abinda ya tada hankalin shugaban kasa Janar Murtala wanda ya tura tawaga ta musamman domin rokonsa ya dawo Najeriya da kuma alkawarin cewar gwamnati za ta kula da shi a matsayinsa na tsohon shugaban kasa tare da ba shi hakkokinsa, amma Gowon ya basu hakuri, ya ce zai ci gaba da zama a can, domin har ya fara karatun jami'a.
Dangiwa ya ce lokacin da yake rike da kujerar gwamnan Kaduna, ya ziyarci gidan su Gowon dake Wusasa a Zaria, a shekarar 1987 tare da Sufeto Janar na 'Yan Sanda a lokacin Gambo Jimeta, inda suka samu mahaifiyar Gowon a dakin ta na laka, inda aka haife shi.
Tsohon gwamnan ya ce a dakin babu komai sai gadon vono da kujerar katako wanda Gambo ya zauna, ya yin da shi kuma ya zauna a kan buhun masara, ita kuwa kanwar tsohon shugaban ta zauna a tabarma, mahaifiyarta kuma a kan gado.
Tsoffin shugabannin Najeriya Janar Yakubu Gowon da Muhammadu Buhari a London © Buhari SallauDangiwa ya ce abin mamaki a lokacin kanwar Gowon na hura wuta da itace domin soya musu kosai, abinda ke nuna shugabanci na gari da Najeriya ta gani a wancan lokaci wanda ya zama abin koyi, sabanin halin da ake ciki yanzu wanda ke bai wa shugabanni damar sauya rayuwarsu da zaran sun hau karagar mulki.
Tsohon gwamnan ya ce abin takaici shugabannin yanzu sun kauce hanya wajen sanya kan su a gaba maimakon jama'ar kasa, ya yin da wasu da dama suka zarme da son duniya, sabanin shugabannin irin su Gowon wanda bayan kwashe shekaru 9 a karagar mulki ko gida guda bai mallaka ba.
Dangiwa ya ce wannan hali na gudun duniya ya sanya shi kai ziyara da dama Wusasa domin nunawa masu aiki da shi irin rayuwar da iyalan Gowon ke yi duk da zaman sa shugaban Najeriya na dogon lokaci.
A karshe, tsohon sojan ya bukaci shugabannin yanzu da su dinga koyi da irin rayuwar shugabannin Najeriya na farko wadanda a koda yaushe su ke sanya gaskiya da kuma tsoron Allah a gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI