Jamus ta bada yuro miliyan 24 don tallafa wa waɗanda ambaliya ta shafa a Najeriya

Jamus ta bada yuro miliyan 24 don tallafa wa waɗanda ambaliya ta shafa a Najeriya

Sanarwar ta ce Jamus ta  na bayan Najeriya da sauran ƙasashen Afrika a duk wani lokaci na jarabta, duba da yadda taimaka wa waɗanda ke cikin yanayi na buƙata na daga cikin manufofinta na hulɗa da ƙasashen waje.

Jamus ta ce duba da cewa wannann ambaliyar ta cimma matsalolin ƙarancin nau’uka abinci masu gina ciki da ake fuskanta a waɗannan yankuna, yaƙi da waɗanan matsaloli na daga cikin abubawan da za a bai wa fifiko da wannan gudummawa.

Gudummawar baya-bayan nan ta kai jimillar  kuɗaɗen tallafin jinkai da Jamus ta bada a yankunan Sahel da tafkin Chadi zuwa yuro miliyan 100.

Ambaliya a yankunan Sahel da tafkin Chadi, ciki  har da Najeriya sun haddasa gagarumar matsalar jinƙai a cikin makwannin da su ka wuce.

Baya ga gudummawar jinkai, Jamus ta sha bai wa yankin tafkin Chadi gudummmawa a shirye-shirye dabam-dabam, da su ka shafi haɗin kai da ci gaba, waɗanda darajarsu ta kai miliyoyin yuro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)