Baturen zaɓe, kuma shugaban jami’ar kimyya da fasaha ta Minna, Farfesa Farku Adamu Kuta ne ya ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Okpebholo ya samu ƙuri’u dubu 291 da ɗari 6 da 67, inda ya kada abokin hamayyarsa na kud-da kud, Asue Ighodalo na jam’iyyyar PDP, wanda ya samu kuri’u dubu ɗari 247 da ɗari 2 da 74. Ɗan takarar kjam’iyyar Labour kuwa ya samu kuri’u dubu 22 da ɗari 7 da 63.
Alƙalumma sun nuna cewa APC tana kan gaba a ƙananan hukumomi 11, a yayin da PDP ta lashe ƙuri’u mafi yawa a ƙananan hukumomi 7.
Jam’iyyar APC ta lashe zaɓe a ilahirin ƙananan hukumomi 6 na mazaɓar ɗan majalisar datttawa ta Edo ta arewa, da kuma ƙananan hukumomi 2 daga cikin 5 na mazaɓar ɗan majalisar dattawa ta Edo ta tsakiya.
Bugu da ƙari, APC ta ci zaɓe a ƙaramar hukumar Esan ta tsakiya, inda ɗan takaranta, Monday Okpebholo ya fito, a yayin da PDP ta lashe zaɓe a ƙaramar hukuma Esan ta arewa maso yamma, da Esan ta arewa maso gabas inda ɗan takaranta, Ighodalo ya fito.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI