Jami'an tsaron Najeriya sun hallaka 'dan Bello Turji a Zamfara

Jami'an tsaron Najeriya sun hallaka 'dan Bello Turji a Zamfara

 

Majiyoyi da dama a yankin sun tabbatar da labarin harin da sojojin suka kai a kan gangamin 'yan ta'addan dake kusa da Shinkafi wanda ya kai ga hallaka wasu daga cikin su.

Wata majiya ta ce cikin wadanda suka samu raunuka har da shi kan shi Bello Turji wanda aka dade ana nema ruwa a jallo.

Ko a karshen makon jiya rahotanni daga Shinkafi sun ce Turji ya addabi mutanen yankin Shinkafi da kai hare hare yana garkuwa da mutane, kuma cikin mutanen da ya kwashe harda wasu da aka samu a Masallachi suna salla su 13.

Wani mazaunin yankin Dr Suleiman Shuiabu Shinkafi ya tabbatar mana da aukuwar lamarin da kuma nasarar da yace sojoji sun samu.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da 'yan ta'adda suka hana zaman lafiya na sama da shekaru 10, kuma cikin kwamandodin har da Bello Turji wanda 'dan assalin yankin Shinkafi ne da ya yi kaurin suna wajen kai hari yana kashe mutane da kuma garkuwa da wasu domin karbar fansa.

Turji na daga cikin 'yan ta'addan da suke sanyawa garuruwa harajin kariya da kuma tilastawa jama'a yi musu aiki a gonakinsu.

Sojojin Najeriya sun dade suna bayyana nemansa ruwa a jallo da kuma kai masa hari yana tsallake rijiya da baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)