Jami’an tsaro sun mamaye fadar Sarkin Kano da fadar Bichi a Najeriya

Jami’an tsaro sun mamaye fadar Sarkin Kano da fadar Bichi a Najeriya

Wannan ya biyo bayan wasu bayanai da ke nuna cewa sarki Muhammadu Sunusi II zai ziyarci garin domin bikin naɗin sabon hakimi.

To sai dai jami’an tsaro sun tare ƙofar fita daga masarautar ta Kano da duk wata hanya da za ta sada mutum da masarautar.

Babu cikakken bayani daga jami’an tsaro kawo wannan lokaci kan matakin, sai dai rahotanni sun nuna cewar sun mamaye masarautar ne da nufin hana sarki Muhammdu Sunusi II zuwa naɗin hakimin Bichi.

Bayan mamaye masarautar da jami’an tsaro suka yi a yau, tuni sarki Muhammadu Sunusi II ya fito zaman fada kamar yadda ya saba daidai lokacin da jami’an suka yiwa fadar ƙawanya.

Fadar Bichi Fadar Bichi © RFI Hausa

A garin Bichi kuma tuni jami’an tsaro suka mamaye fada tare da fara sintiri a ciki da kewayen garin tun da sanyin safiyar yau.

Alumma a garin na Bichi na gudanar da harkokinsu a yau juma’a da babbar kasuwar garin ke ci cikin tsauraran matakan tsaro.

Sai dai wata majiya ta shaidawa RFI Hausa cewar tuni aka gudanar da zanga-zanga a garin dangane da batun naɗa sabon hakimin.

Rikicin masarautar Kano dai na ƙara ɗaukar sabon salo tun bayan soke masarautu da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya yi, abin da ya sa ake ta samun hukunce-hukuncen kotuna masu cin karo da juna kan sarauta  a jihar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)