Jami’an tsaro sun karbe iko da sakatariyar Jam’iyyar PDP da ke Abuja

Jami’an tsaro sun karbe iko da sakatariyar Jam’iyyar PDP da ke Abuja

Rahotanni da kuma hotunan bidiyon da suka karade kafofin yada labarai da kuma intanet sun nuna yadda tawagar ɗaya daga cikin masu ikrarin zama Sakataren jam'iyyar tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoyes suka karya kofar shiga wajen taron da kuma tada hatsaniya.

Bayanai sun ce magoya bayan Anyanwu da karfin tuwo suka fitar da Ude-Okoye da kotu ta tabbatar a matsayin halastaccen Sakatare daga ɗakin taron, yayin da jami'an ƴan sandan da ke ƙofar shiga taron suka zuba ido suna kallo.

A ranar 20 ga watan Disambar bara kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da Ude-Okoye a matsayin halastaccen sakataren, yayin da ta tuɓe Anyanwu daga kujerar.

Yanzu haka sojoji da ƴan sanda tare da jami'an tsaron civil defence ke gadin ofishin domin tabbatar da tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)