Jami’an ofisoshin jakadancin Najeriya a ƙasashe 109 na rayuwa ba albashi- Rahoto

A cewar bayanan jami’an da yawansu ya kai 450 da ke yi wa Najeriyar aiki a ƙetare yanzu haka na cikin mawuyacin hali sakamakon rashin kuɗaɗen da za su yi amfani da su wajen biyan hayar gidajen da suke ciki ko kuma kuɗin makarantun ƴaƴansu da sauran lamurran yau da kullum.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar Kimiebi Ebienfa ya tabbatar da halin da ake ciki inda ya ce ma’aikatar na sane da halin da jami’an ofisoshin jakadancin na ƙetare ke ciki game da matsanancin rashin kuɗi sakamakon gaza biyansu albashin watanni.

A cewar Ebienfa, yanzu haka suna aiki tuƙuru don warware wannan matsala, a wani yanayi da ake fargabar sabuwar dokar da shugaba Bola Tinubu ke shirin sanyawa hannu kowanne lokaci daga yanzu ta iya shafar tsarin kuɗaɗen da ake kashewa kan manufofin Najeriyar na ƙetare ciki har da ofisoshin jakadancin.

Tsagin dokar da ke fatan rage kuɗaɗen da gwamnati ke ɓarnatarwa wanda majalisa ta sanyawa hannu a Najeriyar, na da nufin rage yawan kuɗin da ake warewa ma’aikatu da sauran sassan gwamnati ciki har da ofisoshin jakadanci, waɗanda ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar harkokin waje.

Wasu alƙaluma sun nuna cewa cikin shekaru 4 da suka gabata, ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta kashe kuɗin da yawansa ya kai Naira biliyan 251 da miliyan ɗari 7 da 1 a abin da ya shafi albashin ma’aikata kaɗai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)