Jami'an Hisba za su dawo da sumame kan gidajen caca bayan hukuncin kotun ƙoli

Jami'an Hisba za su dawo da sumame kan gidajen caca bayan hukuncin kotun ƙoli

Hukuncin kotun na jiya kai tsaye ya mayar da dokoki masu alaƙa da caca ko makamantan batutuwan ƙarƙashin kulawar dokokin jiha wanda za su yi hukuncin da zai zo dai dai da al’adu ko addininsu.

Jihar Kano na sahun jihohin Najeriya 12 da dokokin addinin Islama ke da ƙarfi matuƙa duk da cewa a wasu batutuwan suna tafiya kafaɗa da kafaɗa da dokokin ƙasa baki ɗaya ƙarƙashin tanadin kundin tsarin mulki.

Babban daraktan hukumar Hisba a jihar ta Kano Abba Sufi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa tabbas za su dawo da sumame kan gidajen caca lura da cewa haramtaccen lamari ne bisa dokokin jihar.

Ko a watan jiya jami’an hukumar ta Hisba sun kai sumame wasu shagunan cacar wasannin ƙwallon ƙafa a jihar ta Kano bisa tuhumarsu da ɗabbaƙa caca a jihar wanda ke matsayin haramtaccen lamari.

Sai dai bisa tilas Hisba ta saki dukkanin mutanen da ta kama bayan da hukumar kula da lamurran caca ta ƙasar ta bayyana cewa jami’an basu da hurumin kamen ganin cewa caca halastaccen lamari ne ƙarƙarshin dokar ta 2005.

Wannan batu ne ya kai ga sake zama kan dokar wadda kai tsaye kotun ƙolin Najeriya ta kawar da dokar tare da baiwa jihohi wuƙa da nama kan lamurran da suka shafi caca.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)