A cewar sanarwar da kakakin rundunar Babawale Afolabi ya fitar a yammacin jiya Talata, lamarin ya faru ne a garin Farin Kasa da ke kusa da ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Sanarwar ta ce tawagar na kunshe ne da manyan jami’ai 71 da suka fito daga sassan rundunar daban daban, lokacin da mayaƙan masu iƙirarin jihadi su sama da dari 2 suka kai musu hari, a lokacin da suke dawowa daga mahaƙar ma’adinai.
A cewar sanarwar, duk da kwanton ɓaunar da aka yiwa jami’an na Civil Defence, sai da suka samu nasarar kashe sama da mayaƙan masu tada ƙayar baya 50, a musayar mutar da suka yi.
Kakakin rundunar ya kuma tabbatar da cewa jami’ansu 7 sun samu raunuka, inda yanzu haka suke samun kulawa a wani asibiti da ke cikin garin Kaduna, sannan wasu 7 kuma sun ɓace inda ake ci gaba da nemansu.
An dai tura da tawagar rundunar Civil Defence ne don sanya ido tare da samar da kariya ga turakun layukan wutar lantarki, sakamakon yawaitar hare-hare da lalatasu da ake yi, wanda ke haifar da katsewar wutar lantarki a faɗin ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI