Jagoran ƙasar Yarbawa ya caccaki Tinubu

Jagoran ƙasar Yarbawa ya caccaki Tinubu

Adams da ake yi masa kirari da Aare Ona Kakanfo na Ƙasar Yarbawa, ya caccaki shugaba Tinubu kan matakan da ya ɗauka a ɓangaren man fetur, inda ya ƙara farashin litar man a daidai lokacin da al'ummar ƙasar ke shan wahalar tsadar rayuwa.

Ya kuma buƙaci shugaba Tinubu da ya sauya halin da ƴan ƙasar ke ciki, yana mai cewa, lokaci na ƙure masa.

A cikin wata buɗaɗɗiyar wasika da Adams ya aike wa shugaba Tinubun, ya ce masa,

A lokacin da ka ƙaddamar da tafiyar siyasar'Emilokan' gabanin zaɓen 2023, da dama daga cikin ƴan Najeriya sun ruɗu da cewa, a matsayinka na ɗan demokuraɗiyya, za ka yi bajinta fiye da Muhammadu Buhari, wanda soja ne da ya tsananta talauci a tsakanin  ƴan Najeriya tare da ƙara rashin tsaro tsakanin 2015 zuwa 2023

Jagoran na al'ummar Yarbawa ya ce, matakin gwamnatin Tinubu na tsauwala farashin man fetur ya nuna ƙarara cewa, shugaban ba ruwansa da halin da ƴan ƙasar ke ciki.

Adams ya ƙara da cewa, mutane da dama sun yi ta yi masa matsin lamba don ganin ya janyo hankalin shugaban, bayan an zarge shi da yin gum da baƙinsa gabanin aike wa da wasiƙar.

Wannan na zuwa ne bayan ƙarin farashin man daga naira 650 zuwa naira 1000, yayin da wasu gidajen man ke sayar da shi fiye da dubu 1000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)