'Dan majalisar jihar Sokoto Hon Shuaibu Gwanda Gobir ya tabbatarwa RFI Hausa da rasuwar a tattaunawar da aka yi da shi yau da rana.
Gobir ya ce a kokarin da suke na kubutar da Sarkin wanda hotan bidiyon shi ya bayyana sanye da riga jina jina ya gamu da koma baya ne saboda rashin samun irin babur guda daga cikin babura guda 5 da 'yan bindigar suka bukata tare da tsabar kudi naira miliyan 60.
'Dan majalisar yace su iyalan Sarkin sun tara kudin, ya yin da kuma a bangare guda Gwamnan Sokoto ya bada umarnin cewar a bada diyyar, amma safiyar yau labari ya ishe su cewar Sarkin ya rasu jiya da la'asar.
Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu © GuardianGobir ya ce ya samu labarin rasuwar ne daga Sarkin Kudun Sokoto da Dan Madamin Shinkafi da suka kira shi yau da safe.
'Dan Madamin ya ce ya kira shi ne domin kar su kai kudin fansar domin labari ya ishe su cewar Sarkin ya rasu tun jiya a dabar Halilu Sububu kamar yadda masu shiga tsakani suka tabbatar lokacin da suka je shaida musu cewar ana shirin kawo musu kudin fansar.
Magajin Shinkafi ya kuma tabbatar masa cewar 'dan aiken da ya ziyarci inda Sarkin yake ya ga gawarsa a wurin 'yan bindigar a yammacin jiya, saboda haka babu dalilin biyan kudin fansar da suka tattara.
Gobir ya ce gawar Sarkin na Kubuta dake yankin Goronyo a sansanin 'yan ta'addan da suka yi garkuwa da shi tare da 'dan sa.
Ya zuwa yanzu dai babu labarin halin da 'dan Sarkin Gobir Kabiru wanda ke tare da shi lokacin da aka kama su yake ciki, yayin da iyalan Sarkin ke duba hanyar da za su bi domin karbo gawarsa da kuma Kabirun.
Hon Gobir ya bayyana matukar bacin ransa da yadda gwamnati da hukumomi suka yi sakaci har ya kai ga rasa ran Sarkin duk da yadda bidiyonsa ya bayyana a kan yadda 'yan bindigar suka sanya sarka a hannaye da kafafuwan Sarkin suna kuma dukansa ba tare da kaukautawa ba.
'Dan majalisar ya ce iyalansa sarkin na cikin tashin hankali a wannan lokaci, kuma ba za su taba manta abinda aka musu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI