IPMAN ta ce saukar farashin ya zama dole saboda ragin da matatar mai ta Dangote ta yi ga dillalan man, da hakan zai bayar da damar ƴan kasuwar su sayar da lita kan Naira 935 a faɗin ƙasar.
Shugaban ƙungiyar IPMAN a matakin ƙasa, Maiganfi Garima ne ya bayyana hakan a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, a Abuja babban birnin ƙasar, har ma ya yabawa Dangote bisa wannan ci gaba da ya kawo.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur da ta ke sayarwa ƴan kasuwa da Naira 70.5, wato daga Naira 970 zuwa Naira 899.50 a duk lita.
Matatar ta ce akwai buƙatar ɗaukar wannan mataki saboda sauƙaƙawa al’umma yayin bukukuwa da hutun ƙarshen shekara, baya ga samun sauƙin farashin sufuri da ragin zai haifar, kuma tuni aka fara ganin tasirinsa a jihar Legas da ke kudancin ƙasar, yayin da ake sa ran ganin sauyi a sauran sassan ƙasar daga gobe Litinin.
Shi ma kamfanin mai na Najeriya NNPC ya rage farashin mansa daga Naira 1,020 zuwa Naira 899 a duk lita ga ƴan kasuwa.
Ana ganin dai rage farashin man da ake ta rige-rigen yi a yanzu ya samo asali ne bisa ga ƙara samun yawan bangarorin da ke samar da mai a ƙasar, baya ga gasar da ke tsakanin kamfanin NNPC, Dangote da kuma ƴan kasuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI