Shugaban masu defo-defo na ƙungiyar, Yahaya Alhassan ne ya bayyana wannan shiri nasu na tsunduma yajin aiki ga manema labarai a Abuja.
Wannan na zuwa ne bayan da NMDPRA na gaza biyan mambobin IPMAN basussukan da suke binta na kuɗaɗensu kusan shekaru 3, bayan da ta yi alƙawarin biyansu kwanaki 40 da suka gabata a gaban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu.
Idan har ba’a shawo kan wannan matsala ba, to hakan ka iya janyo ƙarancin man fetur da tsadarsa a faɗin ƙasar musamman a yankin arewaci, saboda dai na dakonsa da dillalan za su yi zuwa yankin.
Alhaji Musa Yahya Maikifi shi ne sakataren kuɗi na ƙungiyar IPMAN ya yiwa RFI Hausa ƙarin bayani kan haƙƙonkinsu da gwamnati ta gaza biya..
Latsa alamar sauti domin saurarensa...
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI