A cewar IPMAN, an samu saɓanin fahimta tsakaninta da kamfanin mai na Najeriya NNPCL, lura da yadda kamfanin a yanzu ke sayar da mai da matuƙar tsada ga ƴan kasuwa ko kuma mambobin ƙungiyar saɓanin farashin da ya ke sayarwa ga rassan shi da ke sassan ƙasar.
A jawabinsa gaban manema labarai, kakakin yaɗa labarai na ƙungiyar Okanlawon Olanrewaju ya ce kamfanin na NNPCL na son sayarwa da ƴan kasuwar man ne akan farashin dubu guda da naira 10 wanda kuma zai yi musu matuƙar wahala gudanar da hada-hadarshi a wanann farashi.
Tun farko dama IPMAN ta yi gargaɗin yiwuwar tsanantar ƙarancin man a sassan Najeriya saboda abin da ta kira tsauraran matakan na NNPCL ke ɗauka.
Ƙungiyar ta IPMAN ta ce yanzu haka bashin bankuna ya yiwa mambobinta katutu saboda yadda NNPCL ke neman maƙuden kuɗaɗe a hannunsu ta yadda har sai sun ɗora wani adadi kan ainahin ƙudin mansu gabanin iya sayen man.
Kawo yanzu dai kamfanin na NNPCL ya baiwa dillalai da tsirarun ƴan kasuwar damar sayen man kai tsaye daga matatar Ɗangote, a wani yunƙuri na wadata ƙasar da mai, sai dai kawo yanzu ana ganin dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai.
A cewar IPMAN idan har yanayin da ake ciki a yanzu ya ci gaba, ko shakka babu Najeriya za ta faɗa matsanancin halin ƙarancin man fetur.
Sau 4 kenan cikin watanni 16 gwamnatin Najeriya na ƙara farashin man wanda kuɗinsa ya ruɓanya idan an kwatanta da yadda ake sayenshi kafin hawan shugaba Bola Ahmed Tunibu karagar mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI