IPMAN ta nemi matatar Dangote ta rage farashin litar mai a Najeriya

IPMAN ta nemi matatar Dangote ta rage farashin litar mai a Najeriya

Mai magana da yawun IPMAN, Chinedu Ukadike ne ya bayyana buƙatar rage farashin man saboda sauƙaƙawa ƴan ƙasa a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Punch a ƙarshen mako.

Chinedu ya ce kuɗaɗen da ake kashewa wajen samar da mai ya banbanta a kowace matata, sai dai a cewarsa akwai buƙatar Dangote ya ƙara yin nazari game da farashin litar mai da yake sayarwa dillalai.

A watan Nuwambar da ya gabata ne , Matatar man Dangote ta sanar da rage farashin tataccen mai da ta ke sayarwa dillalan man fetur, daga Naira 990 zuwa 970 don gode wa al’ummar ƙasar bisa goyon baya da su ke ba ta, dai-dai lokacin da ake jita-jitar cewa za a ƙara farashin litar man fetur a ƙasar.

Shugaba Bola Tinubu dai yayin taron majalisar zartaswa ta tarayyar Najeriya a ranar 29 ga watan Yuli, ya miƙa buƙatar sayar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida irinsu Dangote da sauransu da takardar kuɗin Naira, abinda majalisar ta amince da shi.

Majalisar ta kuma amince da amfani da matatar Dangote a matsayin hanyar sayar da gangar mai dubu 450 ga matatu da dillalan man fetur na cikin gida da kuɗin Naira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)