Tinubu ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali ne wajen janyo masu zuba hannun jari daga gida da waje a fannin noma da kiwo, domin kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.
Shugaban na wannan batu ne a birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil yayin rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanin JBS guda daga cikin manyan kamfanonin sarrafa nama 3 da ake dasu a faɗin duniya, wanda zai kawo ci gaban harkokin kiwo a Najeriya.
Bola Tinubu ya ce damarmakin zuba hannun jari a fannin ya kai Dala biliyan 2 da miliyan 500.
“Muna ƙokarin sauya yanayin talauci zuwa na yalwar tattalin arziƙi, muna duba kan matsoli domin samar da makoma mai kyau’’ inji shi.
“Wadatar abinci na da matuƙar muhimmanci, a halin yanzu da muke magana akwai yunwa a ƙasarmu, amma duk da haka sauƙi na nan tafe, wanda muke fatan yarjejeniyar nan na daga cikin hanyoyin kawo shi’’.
Wesley Batista, mamallakin kamfanin JBS, ya ce kamfanin shi ne mafi yawan ma’aikata a Brazil, wanda tuni suka samar da kuɗaɗen shiga na Dala bilyan 79 a shekarar 2024 da muke ciki.
Kafin tafiyarsa Brazil, shugaban Najeriyar ya tattara tawagar da zata yi amfani da damar zuwa taron G20, wajen lalubowa da ganawa da waɗanda za su zuba hannun jari a fannin noma da kiwo a ƙasar daga Brazil.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI