Ina cikin koshin lafiya amma wasu na yaɗa cewa na mutu - Obasanjo

Ina cikin koshin lafiya amma wasu na yaɗa cewa na mutu - Obasanjo

Obasanjo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wajen ƙaddamar da tsohuwar hanyar Garage/Oke Fia-Lameco da ke garin Osogbo na jihar Osun, inda ya ce shi da kan shi ya samu labarin da ake yaɗawa kan mutuwar tasa.

Na gani a kafofin sada zumunta ana yaɗa cewa wai na mutu, shi ne nayi gaggawar saidawa ƴaƴana da dangina cewa ba gaskiya ba ne ina raye. Waɗanda suke so na mutu, burinsu ke nan amma har yanzu Ubangiji ya bar ni da raina.

Tsohon shugaban Najeriya ya ce bai san dalilin da ya sa wasu ke masa fatan mutuwa ba, duk da cewa suma ba za su kauce mata ba.

Obasanjo ya nuna rashin jin daɗinsa game da yaɗa irin waɗan nan labarai, waɗanda ya bayyana a matsayin masu ɓata rai da wasu ke amfani da fasaha wajen ƙirƙiransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)