Ƙimar Najeriya na zubewa a idon duniya saboda rashin jagoranci na gari - Rahoto

Ƙimar Najeriya na zubewa a idon duniya saboda rashin jagoranci na gari - Rahoto

A makon jiya ne, Gidauniyar Mo Ibrahim ta fitar da wasu alkaluma game da jagoranci a ƙasashen Afrika, inda aka bayyana Najeriya a matsayin ta 33 wajen iya tafiyar da shugabanci daga jerin ƙasashe Afrika 54, yayin da aka bai wa ƙasar maki 45.7 cikin 100.

Wannan makin na nuna cewa, Najeriya ta samu koma-baya a fannin tsaro da bin dokoki da kare hakkin bil'adama da gina tattalin arziki da kuma ci gaban ƴan ƙasar.

A cikin wata sanarwa da cibiyar ta fitar ta ce, waɗannan alkaluman sun nuna cewa, akwai buƙatar samar sauye-sauye na gaggawa domin maido da ƙimar ƙasar ta hanyar magance matsalolin da ke addabar ta.

Cibiyar ta ce, wannan rahoton tamkar gagarumin kira ne ga gwamnatin Najeriya don ganin ta farka tare da fara gina al'ummar ƙasar ta hanyar inganta tsarin kiwon lafiya da ilimi da bada horo don haɓɓaka basirar ƴan ƙasar, baya ga bunƙasa tattalin arziƙi.

Kazalika cibiyar ta buƙaci gwamnatin Najeriya da ta bada gudunmawa ga kamfanoni masu zaman kansu ta hanyar bullo da tsare-tsaren da za su janyo zuba jari daga ƙasashen ketare tare da bunƙasa ƙananan sana'o'in cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)