Tawagar Super Eagles ta kasance bata da mai horas wa tun bayan da Mai horarwarta, Finidi George ya ajiye aikinsa bayan wasa biyu kacal da ya jagoranci su.
Tuni dai aka bayyana sunan Janne Andersson ɗan Sweden da Herve Renard na Faransa.
Sai dai ana ganin akwai babban ƙalubale ga duk wanda zai karɓi tawagar ta Super Eagles a yanzu, duba da yanda lokaci ke ƙoƙarin ƙurewa la'akari da ana daf da fara wasannin share fagen shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika a watan Satumba.
A ranar 1 ga watan Satumba ne ake sa ran Super Eagles za su koma sansaninta a birnin Uyo domin fara atisaye wasannin neman gurbin shiga gasar AFCON ta 2025 da a cewar jaridar PUNCH Sports Extra.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI