Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kame mutumin ne wanda ya taso daga Habasha tare da sauka a filin jirgin saman Lagos ɗauke da kiogiram 19.4 na hodar iblis da darajarta ta kai dala miliyan 2 da dubu 900 da 3 dai dai da naira biliyan 4 da miliyan 66.
A cewar NDLEA, mutumin mai shekaru 48 wanda ɗan kasuwa ne, ko a bara an kama shi da laifin safarar miyagun ƙwayoyi amma kuma ya biya tara a wancan lokaci don kaucewa zaman kaso.
A wannan karon NDLEA ta ce ta samu ɗan kasuwar wanda ba a bayyana sunanshi ba ɗauke da ƙulli 817 na hodar iblis a ranar 18 ga watan Satumban da muke ciki.
Najeriya mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika, a shekarun baya ta na matsayin babbar matattara ɓatagari da ke aikin safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin ƙasashen kudancin Amurka da nahiyar Turai, sai dai a baya-bayan nan ta rikiɗe zuwa matattarar masu ta’ammali da hodar ta Iblis ko kuma Cocaine.
Wata sanarwa da hukumar ta NDLEA ta fitar ta ruwaito shugabanta Mohammed Buba Marwa na sha alwashin zafafa yaƙi kan masu safarar miyagun ƙwayoyi a sassan ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI