Da yake sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, kakakin hukumar ta NDLEA Femi Babafemi, ya ce jami’an hukumar da ke filin jirgin sama na Murtala Muhammed ne suka kama miyagun kwayoyin.
Ya ce a ranar 12 ga wannan watan ne dai jami’ansu suka kama kwayar tramadol dubu 2 da dari da 18 a ƙarƙashin takalma 13 da za a kai ƙasar Cyprus, a filin jirgin saman Lagos, sannan suka sake kama ƙarin 380 a gidan wanda ya tura da sakon Okenwa Kelvin Uchenna da ke Enugu, a ranar 24 ga wannan watan.
Kwayar Tramadol 2,118 da aka boye a cikin ƙasan takalma 13 da za a kai su ƙasar Cyprus an kama su ne a filin jirgin saman Lagos a ranar 12 ga Oktoban 2024 da kuma ƙarin wasu 380 da aka kwato daga gidan wanda ya aiko da su Lagos, Okenwa Kelvin Uchenna a lokacin wani samame da aka kai gidansa da ke Enugu a ranar Alhamis 24 ga Oktoba. An kuma samu kuɗi Naira dubu 968 da dari 880 da wata mota kirar Toyota Avalon daga hannun wanda ake zargin.
Haka nan, jami’an hukumar ta NDLE sun samu nasarar kama kwayar tramadol miliyan 26 da dubu dari biyu da 50 da kuma kwalaɓen codeine dubu dari biyar da 8, da dari 4, da kuɗinsu ya kai naira miliyan dubu 16 da miliyan da miliyan dari 683 da dubu dari 8, a lokacin da suke binciken haɗin gwiwa tsakaninsu da jami’an kwastam da sauran jami’an tsaro, kan wasu kwantenoni da ake zarginsu a tashar jiragen ruwa ta Tincan da ke Lagos da kuma Fatakol, a tsakanin ranakun 22 zuwa 23 ga watan nan na Oktoba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI