Hukumar NCC, ta haramtawa ‘yan Najeriya ‘yan kasa da shekaru 18 karbar layukan sadarwa

Hukumar NCC, ta haramtawa ‘yan Najeriya ‘yan kasa da shekaru 18 karbar layukan sadarwa

 

A cewar hukumar ta NCC babban manufar,ita ce kare kananan yara da kuma karfafa tsaron kasa.

Hukumar NCC dai ta dade tana sauya manufofinta na sadarwa domin yakar matsalolin tsaro a Najeriya.

Wayar tafi da gidan ka Wayar tafi da gidan ka (CC) Erik Hersman/Flickr

A shekarar 2021, NCC ta ba da shawarar yin rijistar masu amfani da layukan sadarwa ko wayar tarho inda ta ba da shawarar hana yara kanana a Najeriya samun katin SIM,dokar da ke aiki yanzu haka.

Daya daga cikin jami’an hukumar ta NCC ya ce manufar za ta dora wa iyaye wani gagarumin nauyi a wuyansu na kula da harkokin wayar yaransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)